Assalamu Alaikum Warahmatullahi wa barkatuh.
Zuwa ga iyaye masu daraja.
HUTUN
TSAKIYAR ZANGO (MID-TERM BREAK)
Bayan gaisuwa irin ta addinin musulunci tare da
fatan alheri, kasancewa zango na biyu na wannan shekara yazo tsakiya, kamar
yadda aka sani akan bada hutu na tsakiyar zango. Hukumar makaranta tana sanarda
iyaye cewa daga gobe Alhamis 25/02/2021 za’a tafi hutu wanda za’a dawo ranar
Litinin 01/03/2021, hutun ya hada dukkan bangarorin biyu na safe da yamma.
2.
Bayan kokari da iyaye suke yi na ganin sun kawo yaransu makaranta akan lokaci,
su kara himma akan hakan.
3. Ana kara tunatar da Iyayen da basu biya kudin
makaranta ba cewa suyi kokari su biya daga nan zuwa Lahadi 28/02/2021 domin
daliban da aka yiwa register ne kawai za su samu damar cigaba da karatu daga
Litinin 01/03/2021.
4. Muna maraba da dukkan wani korafi ko kuma shawarwarin da
zasu taimakemu domin inganta makarantar. Daga karshe muna matukar godiya bisa ga
hadin kai da kuke bamu.
Sign
Management
class="separator" style="clear: both;">
0 Comments